Wani tela ne a garin Zaria ya halaka abokin huldar sa har lahira bayan abokin nasa ya bashi dinkin kayan Sallah, har ma ya biya shi kudin dinkin amma baiyi ba.

Shi dai telan mai suna Aliyu Inyasi da ke zaune a Sabon Layin Tudun Wada Zaria ya dabawa abokin huldarsa, Bashir Shehu Ibrahim mai shekaru 20 a duniya almakashi ne wadda hakan tayi sanadiyar mutuwarsa.

Kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito, marigayi Bashir ya tafi shagon Inyasi ne domin ya karbi dinkin sa amma sai rikici ya barke tsakanin su saboda telan bai dinka masa kayan ba.

Kamar yadda wani bawan Allah mai suna Rabiu da abun ya faru a gabansu, yace mutanen biyu dai makwabta ne amma duk da haka Inyasi ya shafa wa idanunsa toka ya dabawa abokin huldarsa almakashi.

''Munyi hanzarin kai shi asibiti amma misalin mintuna 10 bayan afkuwar lamarin sai Bashir yace ga garin ku.

"A lokacin da muke dawowa da gawar Bashir gida daga asibiti, Mahaifin Inyasi tuni har ya kira jami'an yan Sanda kuma ya mika Inyasi garesu tare da yi musu bayanin cewa Inyasi be ya kashe Bashir'' Inji shi.

DPO na rundunar yan Sanda reshen Tudun Wadan ya tabbatar da afkuwar lamarin kuma yace sun mika binciken zuwa ofishin su na jiha domin cigaba da bincike.

Post a Comment

 
Top