Gwamnonin jihohin arewa sun yanke hukuncin saka mafarauta da 'yan banga domin yakar matsalar 'yan bindiga da duk wani nau'in rashin tsaro da ke yankin.
Wannan ya biyo bayan yawaitar kashe-kashe a jihohin Katsina, Zamfara da sauran jihohin yankin, jaridar Daily Trust ta wallafa.
Kungiyar gwamnonin arewa, wadanda suka yi taro ta yanar gizo don sake duba yanayin tsaron yankin, sun samu shugabancin Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong.
Gwamnan ya nuna damuwarsa da yadda rashin tsaro ke ci gaba da ta'azzara a yankin wanda ya kai ga rashin rayuka da kadarori.
Gwamnonin sun yanke hukuncin kafa kwamitin da zai dinga lura da tsaron yankin wanda zai samu shugabancin Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.
Kwamitin ya kunshi gwamnan jihar Zamfara da na jihar Gombe a matsayin mambobi. Kamar yadda wata takarda da daraktan yada labarai da hulda da jama'a na gwamna Lalong, Dr Makut Simon Macham ya fitar a Jos ta bayyana, ta ce gwamnonin sun shirya yakar matsalar tsaro.
Post a Comment