Da yawa daga cikin mata musamman ma Hausawanmu na yau, sun duƙufa wajen amfani da wasu sinadarai don ƙarawa ‘ya’yansu mata ni’ima wajen gamsar da mazajensu. To haƙiƙa, ba zai iya zama laifi in an yi ba, sai dai matsaloli da illa da yake haifarwa bayan an yi amfani da shi ya fi muhimmancinsa yawa musamman ga mace budurwa da ba ta taɓa auren fari ba.

Mata da yawa daga cikin iyaye, sun ma ɗauki wannan hanyar a matsayin sana’a ta neman abin dogaro da kai, sukan kai tallar irin waɗannan magunguna gidajen mata musamman inda ake biki don tallata hajarsu.
Da zarar an ce mace an sa ranar aurenta, to iyaye da kuma ‘yan matan kansu, za su fara zuwa neman taimakon magungunan. Akan ɗauki tsawon lokaci ana haɗa mace, maimakon a bar ta ta tafiyar da kanta a kan irin tsarin da Allah Ya tsara mata da irin waɗannan gamje-gamjen magungunan da ba su da asali wanda nan gaba za a samu rikirkicewar sha’awa domin yamutsa ta ɗin da aka yi da waɗannan sinadarai. Daga cikin ire-iren waɗannan sinadarai akwai:
Na sha da madara ko a shayi
Na dafawa da kaji
Na ci da nama
Na ci da baru
Na mannawa
Illolin da maganin ke haifarwa
Gusar da ni’imar mace na asali da take da shi:

Duk macen duniya, akwai ni’imar da Allah ya mata wajen gamsar da namiji, amma irin ni’ima da mata ke ƙarawa kafin su yi aure na haifar masu da illa wajen gusar da ni’imar da suke da shi na asali. Domin da zarar wannan haɗin magunguna da suka yi ya gushe, to ni’imarta na asali da take da shi ne zai dawo, amma kuma ba lallai ne miji ya gamsu da ita ba. Domin wanda aka yi kafin auren da ma ba mai ɗorewa ba ne kuma babu shi.
Cire wa miji sha’awar matarsa, Da zarar wannan haɗin magunguna da aka yi wa mace kafin ta shiga gidan mijinta ya gushe, to ni’imarta zai ragu da kashi 80% sai na asali da take da shi ya dawo, shi kuma miji ba zai taɓa jin tana gamsar da shi kamar da ba. Daganan sha’awa da yake mata zai fara raguwa, idan aka yi rashin sa’a sai ma ya haifar masa da sha’awan wasu mata a waje.
Shawarwari
A matsayin mace budurwa da ba ta taɓa aure ba, to ki guji duk wasu kayan da za su sanya miki ni’ima in kin sha, domin tun asali irin wadannan magunguna an yi su ne don matan da suka ɗan jima cikin aure kuma zuumar sha’awarsu ta ɗan fara sanyi.
Amma a matsayinki na budurwa kina iya shan ‘ya’yan itatuwa da yawa gab da bikin naki, inda hali ma, kina iya daina cin duk wani abinci illa ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki kaɗai kamar ana sauran sati ɗaya bikin naki.
Haka ma magungunan Musulunci da aka samu ingancin warakarsu daga Manzon Allah SAW, irin su zuma, habbatus sauda, zaitun da sauransu. Waɗannan za su warkar da duk wani rauni ko cikas da ƙila mace ke da shi a lafiyar jiki da ta ruhi gaba ɗaya wajen sanya ni’ima. Mai karatu na iya duba wannan makala da ke bawa mata shawara cewa, ba boka ba malam mallaki mijinki cikin sauki..Ubangiji ya kare mana lafiyarmu baki ɗaya.

Post a Comment

  1. Salamu alaikum Dan Allah Inason Number waya mai wannan site din inda hali Nagode

    ReplyDelete

 
Top