Rahotanni dake shigowa daga kafafen yada labarai da dama sun tabbatar da cewar shugaban R-APC, Buba Galadima, ya gamu da hatsarin mota a hanyarsa ta dawowa daga jihar Yobe inda ya je yiwa dan uwansa ta’aziyyar rasuwar diyar sa.

Galadima na tare da ‘ya’yansa biyu; Sadiq Galadima da Mohammed Galadima, da kuma wasu mutane biyu lokacin da hatsarin ya afku.
Wani jigo a tafiyar R-APC, Emmanuel Sawyerr, dake da kusanci da Buba Galadima, ya ce motar da Galadima ke ciki ta wuntsula sau da yawa yayin da hatsarin ya afku.

Ba a san halin da Buba Galadima ke ciki ba ya zuwa yanzu.

Zamu kawo maku karin bayani....

Post a Comment

 
Top