Neman matan juna ga mabiya kungiyar Hakika ba laifi ba ne, wata sabuwar akida da ta bulla a arewacin Najeriya.

Cikakkun 'yan Hakika za su iya neman matan juna da kuma barin yin sallah da azumi, kamar yadda wani dan kungiyar ya shaida wa BBC.
Ya ce idan dan hakika ya kai kololuwar akidar zai iya yarda wani da ya kai matsayinsa ya nemi matarsa.

"Idan na kai matakin, shi ma ya kai matakin zai iya nema ba wani abu ba ne a Hakika."

A cewarsa, ba haka kawai suke barin sallah ko azumi ko kuma tarawa da mata ba, sai an bi wani mataki da ke ba wa mabiyi damar yin hakan, matakin da suke kira Tarbiyatul Askaru.

Ya ce "duk mutumin da aka ce ya yi Tarbiyatul Askaru zai fahimci kan sa, ya san wane ne Allah. Kuma idan ka yi nisa za ka shafe komai, ka daina ganin laifin komai,"yana jaddada cewa isa wannan matakin yana samar da sauki wajen aikata ibada, kasancewar yin wadannan shika-shikan addinin Musuluncin ba wajibi ba ne.

Post a Comment

 
Top