Ali Nuhu ya karyata labarin da ake yadawa na cewa jarumar Indiya ta wulakanta shi

Fitaccen jarumi Ali Nuhu ya karyata labarin da ake yadawa akan shi na cewa jarumar Indiya ta yi masa wulakanci

- Jarumin ya bayyana cewa wannan labari bashi da tushe bare makama, inda kuma ya bukaci masoyansa da suyi watsi da wannan labari na kanzon kurege

- Idan ba a manta ba makonnin da suka gabata labari yayi ta yawo wanda ke nuna cewa jarumar Indiya ta yi burus ta kyale jarumin bayan ya aika mata sakon murnar ranar haihuwarta

Idan ba a manta ba kwanakin baya mun ruwaito wani labari da muka samu daga jaridar Dabo FM wanda ke nuni da cewa fitacciyar jarumar Indiya Shraddha ta wulakanta fitaccen jarumi Sarki Ali Nuhu a yayin da ya tura mata sakon murnar ranar haihuwarta.

Bayan wani kiran waya da muka samu daga wajen fitaccen jarumin ya bayyana mana cewa wannan labari da ake watsawa bashi da tushe bare makama, ma'ana labarin kafafen sadarwar suka yada a wancan lokacin akan shi labari ne na kanzon kurege.

Ba wannan ne karo na farko da aka fara yada labari na kanzon kurege game da jaruman na Kannywood ba, musamman fitattu irinsu jarumi Sarki Ali Nuhu.

Post a Comment

 
Top