Hanyoyi 14 da su taimaka maka wajen dadewa a fagen saduwa da iyali.

KARANTA WANNAN:

Dalilai 6 da ke sanya daukewar sha’awa ga Mace

Ka Guji Takurawa Kanka Yayin Jima’i

Yawan sanyawa kanka damuwa da takurawa zai haddasa maka daukewar sha’awarka. Ka cire tunaninka daga samun wani abu fiye da wanda zaka iya bayarwa a fagen jima’i, ka sanya a ranka cewa zaka cimma burinka na dadewa ba tare da wata takura ba.

Wasa Kafin Fara Saduwa na da Matukar Muhimmanci

Shigarwa iyalinka kai tsaye ba tare da wani wasan motsa sha’awa ba, na janyo jin zafi sosai ga abokin saduwarka. Saboda babu karancin ruwan maziyyi da zai saukaka shigar azzakarinka a jikinta, ko shigar zakarinsa a farjinki. Don haka ya zamana cewa kun fara yin wasanni na motsa sha’awa, yin hakan na taimakawa wajen dadewarku a wajen jima’i. Ku fara da yan rungume rungume, sunbata, tsotse tsotse da sauransu, hakan zai taimaka wajen dadewarku idan kuka fara saduwa.

Yawaita Saduwa

Yawaita saduwa da iyali na taimakawa wajen sanya mutum ya kware tare da sanin makamar dadewarsa. Kwararru sun gano cewa yawaita yin jima’i na taimakawa wajen dai-daita bugun zuciya, wanda ke sa kwanciyar hankali ga jiki da jiyoyin jini, wadanda ke dakile saurin inzali.

Ka San Bangarorin Sha’awarka

Sanin bangarorin sha’awarka da ke a jikinka na taimakawa ainun wajen bunkasa saduwarka da iyalinka. Wannan kuma na taimakawa wajen baka damar jurewa tare da dadewa yayin da kuke saduwa da iyali.

Ka Bunkasa Kwanjinka

Bunkasa kwanjinka na taimakawa ainun wajen sanya dadewa a wajen jima’i. Za ka iya yin hakan ta hanyar ware ko da mintuna ashirin ne a kowacce rana kana motsa jiki, cin karfe, gudu, tseren ruwa da dai sauran abubuwan da zasu bunkasa kwanjinka.

Ka Rage Shan Kayan Maye

Rage shan kayan maye na taimakawa. Idan har kana so dadewa a saman gado, ya zamana cewa ka rage shan giya, da sauran kayan maye, suna raunata karfin azzakari. Giya na sanya ka zamo mai kasala hakan na da illa wajen tashin gaban namiji. Don haka ga guji shan giya idan kana son faranta ran abokiyar zamanka.

Atisayen Mike Kafafuwa da Hannu

Mike kafafuwa da hanu na taimakawa. Irin wannan motsa jikin na sanyawa kuzarinka ya kasance a jikinka, za ka kasance kullum cikin kuzari. Ka samu wani kebantaccen waje, ko a cikin dakinka ne, ka rinka mike kafafuwanka da hannuwanka ko da na mintuna 20 ne a kowacce rana.

Ka Ci Abinci Mai Gina Jiki

Ka kasance kullum mai cin abinci mai gina jiki. Ire iren wadannan abincin na dauke da sinadaran ‘Amino Acid’ da jikinmu ke bukata domin gudanar da ayyuka yadda ya dace. Cin irin abinci kamar kwai, madara maras kitse, kifi da kaza na taimakawa.

Ka Yi Taka Tsan-Tsan da Nauyin Jikinka

Yin taka tsan tsan da nauyin jikinka na taimaka maka ta kowacce fuska a lafiyar jikinka. Ka san iya adadin kimar nauyin jikinka ta hanyar la’akari da tsawo da kuma kirar jikinka. Idan kuma baka da nauyi, to ka tuntubi likitanka domin dai daita maka nauyin jikinka. Wannan na taimakawa wajen  bunkasa fagen saduwa da iyali.

Kafin Saduwa, Kar ka ci Abinci Mai Yawa

Da yawa na tafka kuskure, sukan rinka cin abinci mai yawa alhalin sun san zasu sadu da iyalansu, cin abinci mai yawa na sanya kasala da lalaci. Don haka, idan har kana son dadewa a yayin jima’inka, to ka rage cin abinci mai yawa.

Ka Dai-daita Tsarin Cin Abincinka

Dai-daita tsarin cin abinci na taimakawa wajen gina kwanki, ka san irin abincin da kake ci. Abinci mai gina jiki na da matukar muhimmanci a sha’anin saduwa da iyali. Ka ci abinci wanda bashi da kitse sosai, ka ci ‘yayan itatuwa, ganyaye da nama. Da hakan ne za ka zamo mai cike da kuzari a kowanne lokaci.

Ka Dai-daita Tafiyar Jinin Jikinka

Dole ne ya zamana cewa jinin jikinka na tafiya dai-dai wadaita idan har kana son dadewa a wajen jima’i.

KARANTA WANNAN: Dabaru 6 da za su bunkasa kuzarin Maza a fagen saduwa da Mata

Za ka iya sanya abokinka zamanka ya rinka yi maka tausa, tare da taba maka muhimman bangarorin sha’awarka, hakan na taimakawa wajen baiwa jikinka damar samar da sinadaran da ke kara lafiyar jima’i.

Ka Samu Isasshen Bacci

Akalla ka rinka yin bacci na awanni 7 zuwa 8 a kowacce rana. Samun isasshen bacci na sanyawa ka ji dadin jima’i fiye da tunaninka, amma gajiya da damuwar da take taruwa a kanka idan ba ka yi bacci ba, na rage sha’awarka. Don haka, mayar da hankali wajen samun isasshen bacci mai makon isasshen jima’i na kaiga samun dadewa a yayin jima’in.

Ka Rage Yawan Gajiyar da Kanka

Yawan gajiya na kashe duk wata sha’awa ta jima’i. Duk lokacin da ka ji cewar ka gaji, to ka huta. Za ka iya samun wasu abubuwan da zasu taimaka maka wajen dawo da yanayinka na jin dadi da nutsuwa.

Post a Comment

 
Top