- Shugaban hukumar tace fina-finan Hausa na jihar Kano Isma'ila Na'abba Afakallahu ya tabbatar da cewa zasu kama Rarara matukar bai je an tantance shi ba
- Afakallahu ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da manema labarai a jihar Kano, inda ake yi masa tambayoyi kan yadda zai tafiyar da masana'antar a wannan karo da ya sake lashe zabe
- An yiwa shugaban tambaya akan dalilin da yasa aka kama Sunusi Oscar 442, ya ce ba zai iya cewa komai a kai ba tunda maganar shi na kotu a yanzu
Shugaban hukumar tace fina-finai na jihar Kano Isma'ila Na'abba Afakallahu ya bada tabbacin kama shahararen mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rararaa matukar bai bi doka yaje shima an tantance shi kamar sauran ba.
Shugaban yasha wannan alwashi ne a wata tattaunawa da yayi da jaridar yanar gizo ta Sarauniya inda ake yi masa tambayoyi akan yadda zai tafiyar da ofishinsa a wannan karo da ya sake hayewa kujerar ta shugaban hukumar tace fina-finai.
An tambayi shugaban dalilin sa na kama Sunusi Oscar duk da ana cewa ba shine mamallakin wakokin da ake zargin shi da saki ba, shugaba ya ce koda yake ba zai ce komai akan batun Oscar ba tunda maganar sa tana kotu amma sun tanadi duk wasu hujjoji da zasu tabbatar da cewar wakokin shine mamallakin su.
Hakazalika an sake tambayarsa menene dalilin da yasa suka kama mawakin Kwankwasiyya Sadiq Zazzabi duk da cewa yaje an tace masa wakar sa, shugaban ya bada amsa da cewa shi Sadiq yaje an tace masa waka amma an bashi gyara ya kuma kin bin umarnin hukuma wajen ciccire abubuwan da aka bukace shi da ya cire a wakar sa ya saki wakar a haka, hakan ne yasa aka kama shi, shima kuma yanzu shari'arsa tana gaban alkali.
Sannan sai dan jaridar ya sake tambayarsa da cewa mai yasa hukumar sa bata kama Rarara ba ko dan abokinsa ne, Afakallahu ya tabbatar da cewa shi aiki na al'umma ba ya duba wata alaka ko kusanci, kowaye yayi ba daidai ba doka zata hau kansa, koshi Rararan yaki zuwa a tantance shi ya gani sai an kama shi kuma an hukunta shi sai dai in ba zai saki aikin sa a Kano ba.
Post a Comment