Wani yaro dan makarantar sakandare ya hadu da ajalinsa a sakamakon kwarankwatsa da ta fado masa
-Yaron ya yana saman wani tsauni ne tare abokinsa a lokaci da kwarankwatsar ta fado masa ya mutu nan take
Wani yaro ya dan makarantar sakandare ya gamu da ajalinsa a jihar Ekiti a sanadiyar kwarankwatsa da ta fado masa.
Wannan al’amarin ya auku ne a safiyar ranar Asabar 31 ga watan Agusta wanda ya jefa al’ummar Emure cikin halin juyayi da zaman makoki.
Rahoto daga jaridar Vanguard ya ruwaito cewa yaron da abokinsa sun tafi can saman wani tsauni ne bayan da suka sace kwon kazar da ta riga ta fara kyankyasa.
Har ila yau, yaran sun kore kazar daga saman kwayakwan nata ne inda suka kwashe kwayakwan suka shiga soyawa.
Yaron ya hadu da ajalinsa ne bayan ya gama cinye nasa kwan yayin da shi kuma yaron dake tare da shi bai riga ya ci nasa ba kafin aukuwar wannan al’amari na mutuwar abokinsa.
A daidai lokacin da Vanguard ke tattaro wannan labarin, shuwagabannin al’ummar Emure na shirin yin yanke-yanke da gudanar da roko domin ubangiji tsawa ya gafartawa dayan yaron kada yadda kwarankwatsa ta fadowa waccan yaron ta fado masa shi ma.
Post a Comment