Da alama har yanzu akwai tsumammiya tsakanin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa la'akari da yadda gwamnatin Kano ta ja wa hakimai kunne da kowanne ya tsaya a masarautarsa ya yi haye-hayen sallah.
Ana ganin umarnin gwamnan ya ci karo da sanarwar da masarautar Kano ta bayar ta neman dukkanin hakiman kananan hukumomin jihar 44 da su halarci hawan daushe da masarautar ke shiryawa a duk washe garin sallah.
A wata sanarwa daga gwamnatin jihar wadda mai magana da yawun gwamna Ganduje, Abba Anwar ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gwamna Ganduje ya ce "Sabanin wani labari da yake ta yaduwa a kafafen sadarwa na zamani cewar wai a na gayyatar Hakimai gaba dayansu da su je Hawan Daushe a fadar Sarkin Kano, Gwamnatin Jihar Kano ta UMARCI DUKKAN HAKIMAI DA KOWANNENSU YA JE HAWAN DAUSHE A MASARAUTARSA."
Sanarwar ta ci gaba da cewa "Umarnin ya yi bayanin cewa an umarci dukkan Hakiman da ke karkashin Masarautar Kano da su je Hawan Daushe a masarautar Kano din. Dukkan Hakiman da ke karkashin Masarautar Bichi, da su je Hawan Daushe tare da Sarkinsu mai daraja ta daya Alhaji Aminu Ado Bayero."
"Haka nan an umarci dukkanin Hakiman da ke Masarautar Rano da su je Hawan Daushe tare da Sarkinsu mai daraja ta daya Alhaji Dakta Tafida Abubakar (Autan Bawo)." In ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa "An kuma umarci Hakiman da ke Masarautar Karaye, da su je Hawan Daushe tare da Sarkinsu mai daraja ta daya Alhaji Dakta Ibrahim Abubakar II. Sai kuma Hakiman da ke Masarautar Gaya an umarce su da su je Hawan Daushe tare da Sarkinsu mai daraja ta daya Alhaji Ibrahim Abdulkadir."
Ko a lokacin bukukuwan karamar sallah ma sai da gwamnatin jihar ta Kano ta dage hawan daushe da na Nassarawa bisa dalilan tsaro da ta ce ka iya jefa jihar cikin wani yanayi.
Bayanai sun nuna yadda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya so ya tsige Sarki Sanusi a baya amma aka samu wasu masu fada a ji suka daddanne gwamnan.
A watan Mayun 2019 nan ne dai Gwamna Ganduje ya sanya wa wata doka hannu wadda ta amince da tsaga masarautar Kano zuwa biyar, inda aka samu karin sarakunan yanka guda hudu da suka da Rano da Bichi da Karaye da kuma Gaya.
Kirkirar sabbin masarautun ta bar masarautar Kano da kananan hukumomi 10, inda aka karkasa kananan hukumomi 34 a tsakanin sauran masarautun hudu.
Tun dai lokacin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya samu nasarar yin tazarce wa'adi na biyu, bangaren zartarwa da masarautar Kano suka fara takun-saka.
Bangaren zartarwa na zargin Sarki Sanusi da 'shiga harkar siyasa' ko kuma 'yi wa jam'iyyar adawa aiki', zargin da masarautar ta sha musantawa.
Post a Comment