Shamsu wanda ke zama a yankin Sayako hanyar Maitumbi, Minna, ya bayyana cewa ya dauki tsawon watanni yana wannan sana’a sannan kuma yayi nasarar damfarar maza da dama.
Shamsu ya bayyana cewa yana siyar da sabulun wanke bandaki a unguwanni Minna tsawon watanni kafin ya koma wannan sabuwar kasuwanci, wanda a cewarsa yafi kawo kudi amma yana da hatsari.
Da yake Magana a yayin gurfanar da shi kakakin yan sandan Minna, ASP Muhammed Abubakar, yace yan sanda sun kama mai laifin ne bayan sun samu labarinsa.
Da aka nemi sanin dalilinsa na yin wannan shiga sai yace yana so ya dunga samun kudi ne daga mazan da zasu tsayar da shi su nuna suna son sa.
Post a Comment
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.