Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood mai suna Fatima Abubakar wadda aka fi sani da Fati Shu'uma ta fito fili ta bayyanawa duniya dalilan da ya sa ta shiga harkar fim.
Jarumar ta bayyana dalilan na ta ne a lokacin da ake fira da ita a gidan talabijin din nan na Hausa na Arewa24 a cikin shirin Ga Fili Ga Mai Doki na Kundin Kannywood tare mashiryin shirin Jarumi Aminu Shariff.

NAIJ.com ta samu cewa jarumar dai ta bayyana cewa tun kafin ta shiga harkar ta ji ana cewa ana iskanci ne a masana'antar wanda a cewar ta wannan ne ma dalili na farko da ya kara cusa mata ra'ayin ta shiga cikin sana'ar domin ta ganewa idanun ta ko hakan gaskiya ne ko a'a.

Sauran dalilan da jarumar ta zayyana sun hada da samun kudaden kashewa da kuma yin suna da daukaka kamar dai dukkan sauran jarumai

Da aka tamabaye ta ko fim nawa ta fito a ciki sai jarumar ta ce duk da dai suna yawan gaske don har ma ta nema kirgawa amma dai tana kiyasin cewa sun kai 70.

Haka zalika jarumar ta bayyana jarumi Adam A. Zango da Jamila Nagudu a matsayin jaruman da suka fi burge ta tun kafin ma ta soma harkar fim din.

Source - NaijHausaa

Post a Comment

 
Top