Kayan Hadi
1. Fulawa
2. Nama
3. Albasa
4. Attarugu
5. Maggi
6. Gishiri
7. Curry

Yadda ake hadawa
1. Ki kirba danyen namanki mara kitse da albasa, attarugu da maggi ko ki markada su, ki soya naman sama-sama, sai ki zuba curry ki kara maggi idan bai ji ba.

2. Sannan ki kwaba fulawarki ruwa-ruwa ba mai kauri ba, gishiri kadai za ki zuba a kwabin fulawar da corn flour idan kina dashi, sannan ki dora kwaskon tuyan ki akan wuta ki dinga shafa wannan kwabin na ki na fulawar aciki da burushi, ba’a shafa mai a kwaskon.

3. Idan ya yi sai ki dinga cire shi kina ajiyewa a gafe har sai kin gama da fulawar gaba daya ko kuma daidai yadda ki ke so.

4. Sai ki fara debo naman kina zubawa a tsakiyar fulawar, ki ninke ki rufe naman kamar meatpie sannan ki ninko kowanne gefe ya zo tsakiya, ya yi kamar ninkin ‘triangle’ wato mai kusurwa uku, kamar haka🔺

5. Haka za ki yi ta yi, idan kin gama sai ki sa a mai mai zafi kina soyawa.

A ci dadi lafiya

Post a Comment

 
Top