Wani matashi mai shekaru 22 da aka yi wa tiyata a ciki ya koma tamkar mai juna biyu a sakamakon kuskure da aka samu wajen yin tiyatar.
Matashin mai suna Harrison Gbisanya a yanzu haka dai ya na neman taimakon jama’a domin a gyara tiyatar cikin sa ya koma daidai.
Rahotanni sun bayyana cewa an yi wa Gbisanya tiyatar ne a ranar 13 ga watan Janairun shekarar nan a wani asibiti da ke Accra, babban birnin kasar Ghana, a sakamakon ciwon ciki da ke damun shi
Toh sai dai kwanaki kadan bayan an yi masa tiyatar, sai gurin da aka yanka ya fara masa ciwo, tare da kumburi.
Yayin da ya ke magana a wani gidan rediyon kasar, Harrison ya ce likitan da ya yi masa tiyatar da ya ga haka, sai ya bashi magunguna ya kuma yi masa allura akan cikin ya sallame shi.
Tun daga nan cikin ke ci gaba da kumburi
Harrison na rokon jama’a da su taimaka masa domin kuwa ba shi da wasu kudaden da zai koma asibiti.

Post a Comment