Majiyar Arewaswag.com ta ruwaito gwamnatin jihar ta sanar da haka ne ta shafinta na Twitter, inda tace ta dauki wannan mataki ne sakamakon karar harbe harbe da aka jiyo daga cikin kasuwar, don haka aka rufe kasuwar don gudun asarar rayuka da dukiya.
Shi ma shugaban hukumar mulki na Aare Laatosa na jihar, Adekunle Oladeji ya bayyana cewa wannan mataki na rufe kasuwar ya zama wajibi don gudun yaduwar rikicin zuwa wasu sassan kasuwar da sassan jihar ma gaba daya.
Post a Comment
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.