Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman a kan shafukan zumunta da kafofin watsa labarai, Femi Adesina ya bayyana cewa shugaban kasar zai sanya hannu a kasafin kudin 2018 a mako mai zuwa.
Femi ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugabn kasa kan makomar taron bangaren zartarwa da aka gudanar a ranar Laraba, 13 ga watan Yuni, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

NAIJ.com ta tattaro cewa hadimin shugaban kasar ya sanar da manema labarai tare da ministan lafiya Farfesa Isaac AAdewole da kuma na kasuwanci da zuba jari, Okechukwu Enelamah.


A baya NAIJ.com ta rahoto cewa fadar shugaban kasa ta tabbatar da risitin kasafin 2018 daga majalisar dokoki.

A halin da ake ciki Gwamnatin shugaban kasa Buhari na cigaba da farautan barayin gwamnati da ake zargi da wawure kudin kasa a lokacin da suke rike da kujerar mulki.

Hakan ya biyo bayan samun wata mai shari'a akan gaskiya da akayi, yanzu haka ta tura tsoffin gwamnoni biyu gidan yari.

Post a Comment

 
Top