Fitaccen mai bada umarni a fina finan Hausa da ake yi ma inkiya da Kannywood, Aminu S Bono ya bayyana damuwarsa da yadda ake yawan fito da manyan jarumai Mata a kusan kowanni Fim, wanda ya bayyana hakan a matsayin wata babbar kalubale, inji rahoton Rariya.

Majiyar Arewaswag.com ta ruwaito Bono yana kokawa akan cewa akwai karancin sabbin jarumai Mata, inda yace hakan ne ya sanya tsofaffin jarumai irinsu, Jamila Nagudu, Fati Washa, Aisha Tsamiya, Hadiza Gabon da sauransu yin kane kane a masana’antar.

Darakta Bono ya cigaba da cewa kamata ya yi ace tsofaffin jaruman sun koma fitowa a matsayin iyaye saboda girma ya fara kamasu, amma saboda karancin sabbin jini ya sa duk an bi an raja’a akansu, sai dai yace sun fara kulla kulalliyar yadda zasu yi musu juyin mulki da sabbin taurari.

“A yanzu muna fara fito da sabbin jarumai Mata, da suka hada da Zee Preety, Amal Umar, Bilkisu Shema, Zulaihat Ibrahim, Maryam Yahaya da sauransu, ta hanyar fito dasu a bidiyon wakoki da ban a fim ba, wannan ya taimaka wajen haska su.” Inji shi.

Da yake amsa tambayar ko rashin ganinsu Jamila Nagudu a Fim zai kawo nakasu ga amsuwar Fim, sai yace “Su ma kafin su zo, su Fati Muhammad ne ke haskawa, kuma zuwan nasu ya kawo musu cigaba”.

Ya cigaba da cewa yanzu an wuce lokacin da mata masu zaman kansu ke shigowa Fim, don kuwa a yanzu a cikin Mata goma da zasu yi rajistan fara Fim, za’a iya samun bakwia daga cikinsu masu digiri ne ko kuma suna cikin karatun digirin.

Post a Comment

 
Top