A Jamhuriyar Nijar, an kammala azumin watan Ramadan, bayan shaida ganin jaririn watan Shawwal cikin garuruwa da dama a kasar.
Da maraicen ranar Laraba ne al'ummar kasar suka kai azumi na 29, kuma a yau sun wayi gari ranar karamar sallah inda za a fara bukukuwan sallar.
Rahotanni sun ambato fira ministan kasar, Birji Rafini, na bayyana sanarwar ganin watan a ranar Larabar.
Wasu daga cikin al'ummar kasar da BBC ta tattauna da su sun bayyana farin cikinsu a kan kammala azumin lafiya.
Yayin da wasu kuma suka ce, sallar ta zo musu da ba dadi, saboda matsin tattalin arziki, da kuma ranar da aka kwalla a cikin watan azumin.
'Yan kasar ta Nijar sun ce, da dama daga cikin al'ummar kasar ba su dinka kayan sallah ba, sai dai za su wanke tsoffin kayansu ne su je sallar idi.
Suma wasu teloli a kasar da BBCn ta tattauna da su, sun ce gashi sun an kawo musu dinkuna har ma sun dinka, amma masu su ba suzo sun dauka ba, saboda rashin kudin dinkin da za su biya.
Telolin suka ce, hasali ma, wasu daga cikin wadanda suka kai musu dinkin, kance musu su taimaka su sayar da kayan, za suzo su karbi kudin.
Al'ummar kasar ta Nijar dai sun ce anjima ba a shiga matsi na tattalin arziki ba a kasar, kamar wannan lokaci.
A ranar 16 ga watan Mayun 2018 ne, al'ummar kasar ta Nijar suka fara azumin watan Ramadan, lamarin da ya sha bam-ban da na makwabciyarta wato Najeriya, inda aka fara azumin a washegarin ranar da Nijar din ta fara.
Karin bayani
Batun fara azumi da ajiye shi yana yawan jawo ce-ce-ku-ce a kasashen duniya musamman a Najeriya.
Ramadan dai wata ne da Musulmi suke kauracewa ci da sha da kuma jima'i daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana, inda suke matsa kaimi wurin ibada da addu'o'i.

Post a Comment