Hakika jima’i hanyaa ce ta samuwar Dan Adam wacce Allah S.T. ya samar da ita domin ci gaban rayuwa da kuma yaduwar al’umma.
Masana ilimin jima’i sun tabbatar cewa yin jima’i ko wacce rana na karawa mutum lafiya.
Ko shakka babu yayin jima’i akwai sinadaran da suke gaurayar juna da kuma gina sassan jikkuma dama kashe cuttuka masu warkewa ta hanyar jima’i kawai, amma fa idan abokan jima’in lafiyayyu ne.
Duba da haka ne wannan kafa ta Kunnen Ka NAWA ta kawo muku nazarin abubuan da zasu gina muku jiki domin samar da zuriyya mai karfin dakin ginin halitta.
1)Ridi
Ta yiwu ka yi mamakin mun ambaci ridi, to ba abin mamaki game da haka don kuwa masana sun tabbatar da cewa yana kunshe da sanadarai na zinc da ke habaka yawan maniyyi ga namiji wanda hakan ke kara masa sha’awa.
2) Kankana
Wani bincike da aka gudanar a shekara ta 2008, ya nuna yadda kankana ke kara kuzari ga namiji, saboda wasu muhimman sanadaran da ta ke kunshe da su, harma wasu sukan misalta ta da irin magungunan jima’i da wasu ke sha.
3. Barkono/Yaji.
Wasu ba su san dangantakar gudanuwar jini a jikin dan-adam da jima’i ba. Yadda al’amarin yake yayin da sha’awar mutum ta motsa, hanyoyin jini da ke jikin al’aurarsa sukan bude sai jini ya kwarara, hakan ya ke sanya al’aurar ta sa yin karfi har ya samu damar gabatar da jima’i ba tare da matsala ba.
To shi barkono yana da sinadaran da suke aiwatar da irin wannan aiki a jikin dan-adam. Amma ba ana nufin mutum ya debi yaji ya sha ba, a’a zai hada shine da abinci. Haka nan kuma ana fadakar da mutane wajen takaita amfani da shi,musamman ga wadanda idan sun ci da yawa zai haifar musu da wata matsalar.
4. Citta
Ita ma citta tana aiki ne kwatankwacin na yaji. Kamar yadda yaji ke taimakawa wajen kwararar jini zuwa ga al’aura namiji, haka ita ma ta ke yi. Sai dai kari akan na barkono ita tana kara lafiyar hanyoyin jinin.
Post a Comment