Sitti Hikmawatty, wacce ke a matsayin babbar kwamishiniyar lafiya ta kasar Indonesia, ta bayyana cewa mace za ta iya daukar ciki ba tare da ta yi mu’amala da namiji ba, kawai in ta yi wanka a kwamen kurmen (Swimming Pool) da namiji mai zafin maniyy ya saki maniyinsa a ciki.
Kwamishiniyar ta bayyana hakan ne a yayin da ta ke wata ganawa da kafar yada labarai ta Tribun Jakarta.
Bayan da Hikmawatty ta yi jan kunne ga ‘yan mata da su kiyayi daukar juna biyu ba tare da aure ba, Kwamishiniyar ta bayyana wasu hanyoyi da mace za ta iya samun ciki ba tare da ta yi mu’ammala kai tsaye da da namiji ba, ciki wadannan hanyoyi kuwa har da yin wanka a kwamen kurmen da namiji mai zafin maniyy ya sakin maniyyinsa a ciki.
Ta ce: “Akwai wani nau’in maniyy mai karfi da zafi da zai iya samar da ciki ko da kuwa mace a cikin kurmen waka ya shige ta.
“Maza a yayin wanka a kwamen kurme, na iya sakin maniyy a ruwan sakamakon jin dadi, irin wannan maniyy, in aka dace yana da karfi, zai iya zama ciki in har ya shigi mace ta farjinta a yayin wanka,”
Sai dai wani jigo a kungiyar likitocin kasar Indonesia ya musanta yiwuwar hasashen na Hikmawatty, inda ya ce: “Ruwan kwamen kurme da a turance ake kira da Swimming Pool na dauke da sinadarin chlorine, shi kuma maniyya ba zai iya rayuwa a wannan yanayi na sinadarin chlorine ba.”
Wani masanin ilimin lafiya shi ma ya kalubalanci Hikmawatty, inda ya ce: “In ba ki fahimci harkar lafiya ba, bai kamata a ce ki yi jawabi da ya shafi harkar ba. Ya dai fi dacewa a ce ki yi shiru akan ki fadi abinda zai iya jawo rudani.
“Yana da kyau a fahimci cewa ba kowane namiji ne ya ke sakin maniyy ba a yayin wanka a kwamen wanka na swimming pool, kuma ko da an saki maniyyin, shi maniyy ba ya iya rayuwa a ruwan da ke dauke da sinadarin chlorine bare har ya yi iya ya shiga farjin mace, ya kuma samar da juna biyu.
Tuni da Hikmawatty ta bayyana neman afuwarta ga al’ummar kasar ta Indonesia, inda ta bayyana cewa hasashen nata na kashin kai ne kuma ba shi da alaka da bincike ko kwarewarta.

Post a Comment

 
Top