Goro ɗan itaciya ne da ake amfani da shi domin ci, haka nan alama ce ta karrama baƙo yayin bukukuwa da sauran taruka, musamman a al’adun Najeriya da sauran ƙasashen Afrika ya yamma. Bugu da ƙari ana amfani da shi a abubuwan sha domin ƙarin ɗanɗano.
Goro na ɗauke da sinadarai da dama da ake alaƙanta su da amfani kamar:
1] Wartsakarwa: masu cin goro na amfani da shi domin wartsakewa, ƙara kuzari ko karsashi.
2] Maganin bacci ko kasala: saboda sinadarin kafin(caffein) goro na iya rage jin bacci ko kasala.
3] Maganin tashin zuciya: ana amfani da goro domin magance matsalar tashin zuciya, musamman mata.
4] Dankwafe sha’awar abinci: Cin goro yayin jin yunwa na da tasirin rage sha’awar cin abincin ko jin matsananciyar yunwa.
Sauran amfanin goro da ke da alaƙa da lafiya sun haɗa da:
5] Rage raɗaɗin ciwon ɓarin kai (migraine).
6] Kashe ƙwayayyakin cuta a jiki.
7] Temakawa masu ciwon asma(asthma) wajen buɗe hanyoyin numfashi.
Sai dai duk da wannan alfanu da bincike ke alaƙanta goro da shi, bincike ya nuna cewa; baya ga sauran sinadaran da ke cikin goro, goro na ɗauke da sinadarin kafin(caffein) kaso 2 – 3 cikin ɗari.
Kuma bincike ya yi nuni da hauhawar jini bayan cin sinadarin kafin da ke cikin goro. Sai dai hauhawar jinin ya fi ƙarfi ga masu cin goron a karon farko ko kuma masu ci jifa-jifa. Haka nan hauhawar jinin zuwa na wani ɗan lokaci ne da sinadarin kafin zai ƙare a jiki.
Amma waɗanda suka shafe shekara da shekaru suna cin goron, jiki kan jure tasirin sindarin kafin yau da gobe. Saboda haka tasirin sinadarin kafin a kan hauhawar jini na raguwa ne da tsawaitar lokacin da aka daɗe ana amfani da shi.
Sai dai kuma wani bincike ya sake yin nuni da cewa ga masu hawan jini; amfani da goro yayin da ake shan magungunan hawan jini na da tasirin rage aikin maganin, musamman jinsin maganin hawan jini da ke rufe hanyar kalsiyam(calsium) wanda ke temakawa wajen buɗa hanyoyin jini.
Bayan goro, sinadarin kafin na nan a cikin kofi(coffee), lemukan roba/gwangwani da baƙin shayi, har da ma wasu magungunan ciwo kai, mura, da kasala da ake saye a kasuwa.
Daga ƙarshe, mafi kyawun al’amari tsakatsakinsa, saboda haka zai fi kyau a yi amfani da goro yayin buƙata kaɗai, amma ba ya zama ɗabi’ar kullum ba. Sannan ga masu hawan jini, saboda hauhawar jini da sinadarin kafin ke kawowa, da kuma dankwafe tasirin jinsin wancan maganin hawan jini, zai fi kyau su ƙaurace wa cin goro, da sauran abubuwan da ke ɗauke da sindarin kafin.
Wannan bayani ba zai zamo a madadin tuntuɓar likitan ka/ki ba dangane da cin goro ko kafin.
Post a Comment