Wani kwararren likita, Dakta Chinonso Egemba, da aka fi sani da Aproko Doctor, ya bayyana cewa lalle yana da muhimmanci maza, musamman masu amfani da gajeren wanda a ciki kafin su sanya wando, da suke canja gajeren wandonsu samfurin boxers a kalla a kowane kwana biyu.
Dakta Egemba ya nanata cewa, ci gaba da sanya gajeren wando sama da kwanaki biyu ba tare da an canja ba zai haifar da kwayar halitta samfurin Fungi mai cutarwa, wanda zai jaza kaikayi a matse-matsi.
Dakta Egemba ya bayyana cewa wannan nau’in kwayar halitta ta Fungi mai cutarwa ya fi ga mutane da ke gumi sosai a cikin wandonsu, kamar dai masu wasannin tsalle-tsalle ko motsa jiki ko wani aiki na karfi da zai iya haddasa gumi ta ciki.
Nau’in cutar fatar da wannan kwayar Fungi ke haddasawa kuwa shi ne Jock itch ko tinea cruris, wanda ke sanya fatar yankin matse-matsi ya dade ya yi ja, sannan ya dami mutum da kaikayi.
A cewar Likita Egemba, shi bangaren da al’aura ta ke a jikin mutum, yanki ne na jikin mutum da ke dauke da fata mai duhu, da dumi da kuma danshi sakamakon gumi da wajen ke hadawa. Wannan kuwa yakan bawa Fungi damar haifuwa da kuma ninkuwa cikin dan kankanen lokaci.
Wannan shi ne ya sanya ya zama wajibi maza su ke sauya gajeren wando ko kamfai akalla in ba zai yiwu ba kullum, to, ya zama kowane kwana biyu.
Rashin samar da tsaftar da ta dace a wannan bangare na jiki shi ne ya sa za ka ga wasu maza kullum hannunsu na matse-matsinsu suna susa, domin wajen na dadewa, ya yi saba sannna ya yi ta kaikayi.
Post a Comment