1. Lizimtar amfani da ganyen na’a-na’a yana maganin hauka.
2. Shan ta nasa baki ya rinka kamshi koda yaushe shi yasa ake so wanda ya ci wani abu mai sanya warin baki kamar albasa ko tafarnuwa ya sha na’a-na’a bakinsa zai daina warin.
3. Amfani da ita na hana fitowar kurajen fuska idan kuma ya riga ya fito sai a dimanci shafa manta, za’a samu dacewa musamman ga masu maikon fuska.
4. Yin hayaki da busashshen na’a-na’a ayi turare da shi yana sanya kamshin jiki da kuma kanshi ga wurin da aka yi turaren haka kuma idan aka shaki kamshin da hayakin yana maganin mura
5. Shafa danyen ganyen akai na maganin ciwon kai haka kuma idan ana goge hakora da bushashshen shi yana sanya hakora su yi haske.
Post a Comment