1:- Boye talaucinka har mutane sufara tunanin kai me arzikine
2:- Boye damuwarka akan abinda akayi maka har mutane sufara tunanin wannan abin bai dameka ba
3:- Danne bacin ranka a inda aka bata maka rai har mutane su fara tunanin duk a bind a za ayi maka ba zai taba damunkaba
4:- Yin fara’a ga kowa har mutane sufara tunanin bakayin fishi
5:- Zamo na kowa har mutane su fara tunanin baka da abokin fada
6:- Ka taimaki duk Wanda kake tare dashi har mutane su dinga Neman taimako a wurinka
7:- Ka yanka ya zamo na kowa, koda kayan kowa bai zamanto naka ba, ta hakane mutane za suji dadin zama da kai
8:- Ka zamanto mai kawar da kai a kayan wani har mutane su fara tunanin rayuwar duniya bata dameka ba.
Mu kasance masu hakuri da junanmu domin idan mun mutu mu samu kyakkyawan karshe,
Ya Allah kasa mu dace kasa mu gama da duniya lafiya, amin

Post a Comment

 
Top