ALAMOMIN MACE YAR MADIGO; HATTARA MATA
1- Ki Nisanci Duk Wata Qawa Da Zata Dinga Bayyana Miki Tsaraicinta.

2- Kada Ki Yarda Qawarki Ta Yabaki Ta Fuskar Sha’awa.

3- Ki Guji Qawar Da Zata Dinga Rungume ki Da Nufin Wasa.

4- Ki Tsoraci Qawar Da Zata Dinga Kunna Miki Fina-Finan ‘Yan Madugo (Lesbian).

5- Kada Ki Yarda Qawarki Ta Kama Hannunki Na Tsawon Lokaci Don Idan Ta Jima Tana Shafa Miki Hannu , Da Sannu Zata Kai Ga Mabudin Sha’awa Shine Ta Fara Shafa Miki Kirjinki.

6- Ki Nisanci Qawar Da Zata Dinga Yawan Shafa Gashin Kanki.

7- Ki Kauracewa Qawar Da Za ta dinga Yawan Kwanciya Ajikinki Batare da Wani Dalili Ba.

8- Ki Kyamaci Qawar Da A ko da Yaushe Zata dinga Son Ta dinga Ganin Jikin ki , Kamar Kirjin ki Da Bayan ki Zuwa Kasan Marar ki.

9- Ki Rabu da Qawar Da Za ta dinga Yawan Yi Mi ki Kyaututtuka Masu Tsada Ba Bisa Dalili Ba.

10- Ki Bar Qawar Da Take Yawan Jan Ki Zuwa Gidan Qawayen ta Wadanda Bakisan su Ba Kuma Basu da Mazaje Koma Suna da Mazajen ,
Amma Wa ‘yanda Kika ga Suna Yawan Kulewa Cikin Uwar Daka Ko Suke Yawan Tafawa Suna Rungumar Juna , Ko Kwanciya Akan Cinyar Juna
Ko Suke Yawan Cire Tufafinsu Agaban Juna Ko Wanka Tare.

11- Ki Kyamaci Qawar Da Bata da Hira Sai Hirar Mace Yar Uwar ta.

12- Ki Guji Qawar Da Ba ta son Yawan Mu’amala Da Maza Amatsayin Samari Ko Masoya , Amma Ta fi Mu’amala Da Mace ‘Yar Uwarta Matuka
Ainun.

13- Ki Kauracewa Qawar Da Take da Sha’awar Kallon Fina-Finan Batsa Musamman Irin Na Mace Da Mace (Lesbian).

14- Ki Fita Sha’anin Qawar Da Ake Yada Jita-Jitan Tana Madigo (Lesbian).

15- Ki Rabu Da Qawar Da Take Mu’amala Da Qawaye Masu Madigo (Lesbian) Koda Ita Ba ta yi
Domin Kallon Mai yi Ake yi Mata Kema Haka Za’a yi Miki Kallo.

16- Ki Guji Qawar Da Take Zaman Kanta Agidan Da Ta kama Take Haya Kuma Mata Ke Taruwa Agidanta.

17- Ki Fita Sha’anin Qawar Da Ba ta jin Kunyar Cewa Aga-Aga , Na Kirji Ko Baya Ko Kasan Marar Juna.

18- Ki Hakura Da Qawar Da ‘Yan Madigo Ke Burgeta Koda Ita Ba ta yi.

19- Ki Kyamaci Qawar Da Take Yawan Yabon Surorin Jikinki Irin Kirjinki Da Mararki Da Bayanki.

20- Kiyi Tir Ki Kuma Guji Tareda Kyamatar Qawar Da Kuna Haduwa Maimakon Tamiko Miki Hannu Kuyi Musabiha Sai dai Takai Hannu Ta Daki
Bayanki (Mazaunanki) Ko Ta Dan Shafa Kirjinki.

Mata Kuyi Hattara don samun tsira daga wuta Allah yasa mudace..Ameen

Post a Comment

 
Top