Masana sun bayyana cewa, akwai abubuwa da dama da muke aikatawa da zarar an gama cin abinci wanda ke da matsala da illa ga lafiyar jikinmu.
Kadan daga cikin abubuwan nan sune:

1) Shan sigari: Sigari nada sinadarin ”nicotine” wanda ya ke haifar da ciwon daji da huhu. Wannan illa ta sigari tana zama ninki goma idan aka sha sigarin da zarar an gama cin abinci. Har wayau shan sigari bayan gama cin abinci yana hana narkewar abincin da wuri. Idan ya zama dole sai an sha sigarin to a bari sai bayan kamar sa’a 2 (2 hours) bayan gama cin abincin.

2) Cin ‘yayan itatuwa: ‘Yayan itatuwa na dauke da sinadarai da suke daukan tsawon lokaci kafin su narke su bi jikin dan adam. Shan su kafin a ci abinci zai bada damar amfana da sinadaran gina jiki da suke dauke da su. Shan su kuwa bayan gama cin abinci na jinkirta narkewan abinci yana kuma gadar da zafi a zuciya da kuma yawan gyatsa.

3) Barci: Mutane da dama na yawaita yin barci da zarar sun gama cin abinci wanda hakan na sa kumburin ciki kuma yana sa barci na babu gaira babu dalili a lokutan da basu kamata ba. Bincike ya nuna cewa masu yawan yin barci da zaran sun gama cin abinci sun fi saukin samun cutar bugun zuciya (stroke). Yana da kyau a dakata akalla sa’a 2 bayan cin abinci kafin a yi barci.

4) Wanka: Yin wanka da ruwan dumi bayan gama cin abinci yana tsinka jinin jiki wanda hakan na hana jini isa ga tumbin dan adam. Hakan yana kawo cikas ga narkewan abincin da aka gama ci.

5) Shan Shayi: Shayi na da muhimmanci amma shan sa bayan an gama cin abinci yana kawo karancin sinadarin ”Iron” wanda ke iya sanya jiri da rashin kuzari da gajiya, kamata ya yi a sha shayin kafin a ci abinci. Har wayau karancin ”iron” na iya kawo cutar (anaemia)

Post a Comment

 
Top