Tabbas rake na da matukar amfani a rayuwar dan adam, sannan yakan kare jiki daga cututtuka da dama, sannan yakan kare garkuwar jikin mutum daga cututtuka
Zuwa yanzu dai binciken masana ya inganta amfanin rake ga rayuwar dan Adam:

1. Yana kare mutum daga kamuwa da mura da ciwon daji da na sanyi.
2. Yana kara ma garkuwar jiki karfi.

3. Yana kara ruwan jiki musamman ga masu aikin karfi.
4. Yana taimakawa koda wajen sarrafa fitari.
5. Yana kara lafiyar idanu, ciki, hanta da zuciya.
6. Yana gyara fata saboda sinadarin Glycolic Acid da ke cikinsa.
7. Yana kara ma hakora lafiya amman yana da kyau a kuskure baki yayin da aka gama shansa saboda cikin baki akwai bacteria wadanda za su iya amfani da wannan zakin su haifar wa da mutum wata cutar misali (caris) ma’ana tsutsar hakori.
8. Baya da illa ga masu ciwon suga amman kada me zazzabin typhod da ciwon suga ya yawai ta shansa.
9. Rake na maganin yunwa da dai sauran muhimman abubuwa

Mu ci gaba da shan rake

Post a Comment

 
Top