Zahra Indimi, yar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta yi fice a wani sababbin hotunan ta da suka billo. Kyakyawar yar shugaban kasar ta yi shar da ita yayinda ta nada kambu da bakin riga.

Shafin Bighstudios ce ta wallafa hotunan na Zahra a kan Instagram dauke da take daban-daban. Daya daga cikin hotunan na da taken lu’u lu’u da yadda suke walkiya a ko wani yanayi.

An danganta yar shugaban kasar da lu’u lu’u saboda yadda take sheki cikin hotunan. Kuma sannan kalar kayan da ta sa ya dace ta fatar ta.

Duk da cewar ba wani kwaliyyar azo a gani ta kawata fuskar ta da shi ba kana ganinta kasan Allah yayi kyau a wajen.


Mutane da dama da sukayi karo da hotunan sun jinjina ma wanda ya dauke ta domin ya nuna kwarewa a harkar daukar hoto.

Post a Comment

 
Top