Da alama dai rikicin da ake ta yayatawa dake tsakanin manya kuma shahararrun jaruman nan mata na masana'antar Kannywood watau Rahma Sadau da Nafisa Abdullahi ya zo karshe komai ya wuce.
Mun dai fahimci hakan ne ta dalilin wani rubutu da jaruma Rahma Sadau tayi a shafin ta na dandalin sada zumunta na Facebook inda take taya abokiyar sana'ar tata watau Nafisa Abdullahi murna dangane da wani muhimmin ci gaba da ta samu.

Mun dai samu cewa Rahma Sadau din ta yada labarin ne da jaridar nan ta Pulse Nigeriya Hausa ta wallafa mai taken 'Nafisa Abdullahi: Jaruma ta zama jkada' inda ta rubuta 'Congrats sis' a harshen turanci da ke nufin 'ina taya ki murna 'yar uwa' da Hausa.

A kwanan baya ne dai cikin watan Afrilu kungiyar mashirya fina finai na Kannywood suka shiga tsakanin jaruman yan fim din nan su biyu Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon bayan wata arkalla data shiga tsakaninsu.

Shaidan dai ya shiga tsakanin jarumai matan ne a jihar Kaduna yayin da suke bakin aiki wajen shirya wani fim a garin na Kaduna, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Post a Comment

 
Top