Shahararriyar jarumar nan ta wasan fina finan Hausa wadda tauraruwar ta ta dan kwanta watau Zainab Indomie ta ce duk wanda ya kara cewa tana fama da ciwon kanjamau Allah ya isa.

Jarumar wadda a kwanan bayanan nan hotunan ta suka rika yawo ta rame ta tsomale bayan ta sha fama da matsananciyar rashin lafiya mai tsawo.

Arewaswag dai ta samu labarin cewa alokuttan bayan dai da jarumar Zainab Indomie bata da lafiya mutane da dama musamman yan masana’antar fim din sunyi ta tofa albarkacin bakinsu akan rashin lafiyar tata.

Wasu daga cikin jaruman suna tsogumin cewa kanjamau AIDS ko HIV Zainab ta jajibowa kanta wasu kuma suka ce asiri sababbin jarumai mata suka yi mata.

Post a Comment

 
Top