Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da tayi da jaridar The Guardian a karshen makon jiya inda kuma ta bayyana cewa tayi haka ne kawai bisa la’akari da daga inda ta taso da kuma martaba al’ada da addinin yankin arewa.
NAIJ.com kuma dai ta samu cewa da take tsokaci game da korar ta da kungiyar fina-finai tayi, Rahma Sadau tace ita wannan korar ma gaba ta kaita don kuwa yanzu idon ta ya kara budewa kuma ta kara samun wasu damammaki na gudanar da sana’arta a dukkan fadin duniya.
Haka nan kuma jarumar ta bayyana rungumar da tayiwa mawaki ClassiQ da tayi sanadiyyar korar tata a matsayin bangaren aikin ta da bai kamata a tsangwameta ba game da hakan.
Daga karshe ne kuma sai jarumar ta kara jawo hankalin mutane da cewa shifa tsoron Allah a zuciya yake don haka ba dai dai bane ba a rika yi mata kallon ‘yar iska don kawai tana sana’ar ta.
Shin Meye Ra,ayinku Akan Haka
Source:Naij.com Hausa
Post a Comment
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.