Rikicin ya sake barkewa tsakanin ‘yan kungiyar shi’a da ‘yan sanda a karamar hukumar Zaria, jahar Kaduna.


Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan kungiyar na gudunar da taron na su wanda suke kira da suna Ashura a yayin da ‘yan sanda suka kai masu wani haren ba zata domin su dakatar da taron.

Idan za ku iya tunawa Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya hana kungiyar Shi’a gudunar da duk wani taro a jihar bayan rikicin su da sojojin Nijeriya a shekara ta 2015.

A yanzu dai rundunar ‘yan sanda reshen jahar Kaduna ba saki wani jawabi game da lamarin ba tukun.

Ga hotunan a kasa:

Post a Comment

 
Top