Hanan tayi bajakolin basirar da Allah yayi mata na bangaren sana’ar data fi kauna, wato sana’ar daukan hoto.

Wannan bajakolin ya gudana ne garin Abuja, inda ya samu halartan manyan mutane daga ciki da wajen kasar nan, inda Hanan tayi masa taken, ‘Kirkirar Hanan’.

Daily Trust ta ruwaito Ministan watsa labaru, da al’adun gargajiya Alhaji Lai Muhammed ya samu halartan taron tare da Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari.

A yayin bajakolin, Hanan ta bayyana hotuna da daman a al’adun Arewa, sa’annan ta kara ma matasa kwarin gwiwa dasu dage wajen cika burikansu, inji majiyar HAUSAMINI.com. Ga sauran hotunan:

Post a Comment

 
Top