Wata gamayyar tsageran yankin Neja Delta a ranar Lahadi 17 ga watan Satumbar 2017, sun bayyana cewa zasu kalubalanci duk wani yunkuri na son alakantasu da ‘yan kungiyar IPOB, ko kuma lissafa yankinsu a matsayin daya cikin biyafara.

Tsageran sun fadi haka ne a wata takardar manema labarai da suka sake. Takardar ta samu sa hannun Janar John Duku, Janar Ekpo Ekpo, Janar Osarolor Nedam, Manjo Janar Henry Okon Etete, Manjo Janar Asukwo Henshaw da sauran mashahuran tsagera da ake takama da su a yankin na Neja Delta.

A takardar, tsageran na Neja Delta sun gargadi shugaban ‘yan kungiyar ta IPOB, da dukkanin sauran membobinta akan su kiyayi duk wani abu da ya shafi yankinsu na Neja Delta, musamman ma yankunan Jihar Ribas.

A daya bangaren kuma, tsageran sun yi kalubalanci sojojin Nijeriya dangane da ayyana ‘yan Biyafaran a matsayin ‘yan ta’adda. Inda suka sace, hakan ya saba da dimokradiyya. Sannan kuma sun yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari akan ya sakarwa masu fafutukar neman kasar Biyafara mara su fitsara, don a samu wanzajjen zaman lafiya a kasa.

Haka kuma ‘yan tsageran sun mayar da raddi ga tsohon shugaban Kasa Obasanjo, a shawarar da ya bayar ta cewa a yi zaman sulhu da ‘yan biyafaran. Inda suka zarge shi da cewa shi a zamaninsa bai yi sulhu dasu ba, sai da ma yakarsu da yayi, ciki kuwa har da kulle Dokobu Asari da yayi.

Takardar ta ce; “Muna kira ga gwamnatin Nijeriya da ta bar ‘yan biyafara su balle, tunda sun ce sun gaji da zama a cikin Nijeriya. Ko ba komai ba mu fatan a afka cikin wani sabon yakin basasan. Saboda irin wannan yunkurin na ‘yan biyafara ne ya janyo yakin basasan da aka gwabza a shekarun baya. Su kuma ‘yan biyafara, muna gargadinsu da su daina danganta mu da su, saboda mu ba ‘yan biyafara bane.” In ji tsageran.

Post a Comment

 
Top