Akwai abubuwa da yawa wadanda Ma’aurata suke aikatawa a lokacin Jima’insu. Kuma wadannan abubuwan suna da illoli masu yawa dangane da lafiyarsu jikinsu ko addininsu.



Ga wasu ‘yan kadan Zan lissafo:


1. RASHIN GABATAR DA WASANNI KAFIN JIMA’I: Wannan ba daidai bane domin kuwa Manzon Allah (saww) yace “IDAN ‘DAYANKU YAYI NUFIN KUSANTAR IYALINSA, TO LALLAI A SAMU ‘DAN AIKE A TSAKANINSU”.
Sai Sahabbai suka ce “Wanne irin ‘dan aike?” Sai yace “SHI NE SUMBA (KISS) DA KUMA MUBASHARA (RUNGUMAR JUNA).

Rashin gabatar da irin wadannan wasannin yakan haifar da rashun gamsuwar Jima’i. Shi kuwa rashin gamsuwar Jima’i yakan haifar da matsalolin da zasu kawo rabuwar auren.

Yana daga cikin fa’idodin gabatar da wadannan
wasannin, zai sa Maniyyin ita Macen ya gangaro daga ainihin inda yake, sannan kuma za ta samu cikakkiyar gamsuwa.



2. KUSKURE NA BIYU SHI NE TSOTSON AL’AURAR JUNA: Wannan kuskure ne babba wanda ko dabbobi basu yinsa. Duk da cewa babu wata ayah ko hadisi wanda ya fito karara ya yi bayani akan haramcin wannan, to amma Malamai sun yi sabani sun kasu gida biyu akan hukuncin yin hakan, kuma sun raba hukuncin gida
biyu:

Idan har ya kai ga shan Maniyyi to Malaman Malikiyyah da Hanafiyyah sun ce HARAMUN ne. Domin su a wajensu Maniyyi najasa ne. Kuma bai halatta Musulmi ya shigar da najasa cikin cikinsa ba.
Idan kuma Maziyyi ne aka tsotsa, to dukkan Malamai sun ce HARAMUN ne. domin kuwa shi Maziyyi najasa
ne abisa ittifakin Malamai bai daya.

Idan kuma ba a tsotsi Maziyyi ko maniyyi ba, to Malaman da suke bayar da fatawa a Jami’ar Az’har sun ce MAKRUHI NE.

Wasu kuma irin su Nasiruddeen Albaniy sun ce HARAMUN NE duk da hakan.



3. KUSKURE NA UKU SHINE YIN SURUTAI A LOKACIN JIMA’I : Shi ma wannan ba daidai bane. Shari’ar addinin Musulunci ta hana mutum ya rika yin magana a lokacin da yake tsirara.



4. KUSKURE NA HUDU SHI NE RASHIN LULLUBE JUNA DA MAYAFI: Shima wannan ba daidai bane. yin hakan ya yi kama da Jima’in dabbobi kenan.



5. KUSKURE NA BIYAR SHINE RASHIN AMBATON ALLAH KAFIN FARA JIMA’I : Ya kamata Ma’aurata su kula da yin Bismillah tare da karanta addu’ar nan wacce Manzon Allah (saww) yace duk wanda yake karantawa yayin Jima’i da matarsa, to indai aka samu rabo, to shaitan ba zai iya cutar da yaron ba.

Ga addu’ar nan: “BISMILLAHI ALLAHUMMA JANNIBNASH SHAITAN WA JANNIBISH SHAITANA MA RAZAQTANA”.



6. KUSKURE NA SHIDA: idan Miji ya biya bukatarsa, to bai kamata ya gaggauta sauka ba, har sai ita ma matarsa ta biya bukatarta.



7. RASHIN SAUYA YANAYIN KWANCIYA: Shi ma wannan ayar Alqur’ani ta bada damar miji ya sadu da matarsa bisa kowanne irin yanayi. A tsaye ko azaune ko a kwance ko a tsugunne, mutukar dai ba ta dubura
bane. Don haka ya halatta Ma’aurata su rika chanza yanayin kwanciyarsu saboda kara ma juna nishadi.

8. KUSKURE NA TAKWAS SHINE SADUWA A LOKACIN DA TAKE CIKIN JININ HAILA, KO JININ
HAIHUWA : Allah (SWT) ya ce : “KU NISANCI MATA A LOKACIN HAILA. KAR KU KUSANCESU HAR SAI SUNYI TSARKI”.


9. KUSKURE NA TARA SHINE SADUWA TA DUBURA: Shi ma wannan kazanta ce wacce ko dabbobi basu yi. Manzon Allah (saww) ya ce “TSINANNE NE DUK WANDA YA SADU DA MAI HAILA, KO KUMA YA SADU DA
MACE TA DUBURA”.



ZAUREN FIQHU ya kawo wannan ne a matsayin Wa’azantarwa da kuma wayar da kan Ma’aurata. Ba
wai da wata manufar ba. Allah ya ganar damu.

Post a Comment

 
Top