Babban Hafsan soji (COAS), Laftanal Janar TY Buratai ya bayyana amincewar cewa za a kama shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau nan ba da dadewa ba.

Ya ce hakan yayin da yake yaba da Majo Janar Ibrahim Attahiru,babban kwamandan da kuma rundunar sojoji na Operation Lafiya Dole domin kokarin bi umurni neman kama Shekau da rai ko kuma a matattu cikin kwanaki 40.

Kakakin soji, Brigadier Janar Sani Usman, a wata sanarwa da aka nakalto Buratai, yana cewa duk da cewa kokarin neman kama shugaban kungiyar yana ci gaba da kasancewa, Buratai ya ce ya gamsu da himma da kuma kwarewar jami’an.

Kamar yadda Arewaswag.com ke da labari, Buratai ya taya sojojin murna game da galaban da suka samu a kan wasu shugabannin 'yan ta'adda 5 na hannun daman Shekau.

Babban hafsan sojin ya kara da cewa a cikin kwanaki 40, an kashe 'yan kungiyar Boko Haram 82.

Sanarwar ta bayyana cewa babban kwamandan ya bukaci a kara masu tsawon lokacin kama Shekau wanda babban hafsan sojin ya amince.

Source: Naij.com Hausa

Post a Comment

 
Top