Hukumar 'yan sanda ta jihar Jigawa ta bayar da sanarwar cafke wasu makiyaya guda 2 akan laifin kisan abokin hurdarsu a karamar hukumar Gagarawa dake jihar
Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar DSP Abdu Jinjiri, ya bayar da tabbacin cafke wannan makiyaya guda biyu a wata ganawa tare da manema labarai a babban birnin Dutse.

Jinjiri ya ce a ranar Asabar din ta ta gabata, wadanda ake tuhuma masu shekaru 22 da 23 an cafke su ne a wata riga ta fulani dake Gangara.

Ya ce, wannan makiyayan sun yi tarayya wajen lakadawa wani Manu Isa duka da gora har lahira, wanda mazaunin rigar fulani ne ta Maidamisa.


Rahotanni daga shafin VANGUARD sun bayyana cewa, makiyayan guda biyu sun lakadawa Manu duka ne akan wata budurwa, wanda hakan ya sanya jami'an 'yan sanda suka garzaya da shi asibiti bayan sun isa wajen da wannan ta'addaci ya faru, kuma bayan kwana biyu yana jinya ya ce ga garinku nan.

Idan ba a manta ba, a ranar 9 ga watan Satumba, kwamitin tsaro na karamar hukumar Gagarawa ta kaddamar da dokar hana duk wani bikin al'adu na fulani da ake gudanarwa da daddare a yankin.

An samu wannan sanarwar ne daga bakin ciyaman na karamar hukumar Alhaji Ibrahim Ya'u, bayan wata ganawa tare da kwamitin tsaron na yankin, wanda ya ja kunnen makiyaya akan bin wannan doka ko kuma su fuskanci fushin keta doka.

Post a Comment

 
Top