Jaruma Halima Ibrahim a cikin wata fira da tayi da majiyar mu ta bayyana cewa ita dai kam harkar fim ma gyara mata tarbiyya tayi ta kuma maida ta mutunniyar kirki.
Arewaswag.com ta samu dai cewa jarumar da ta bayyana cewa yanzu haka ta fito a fina-finai akalla 20 ta kuma ce harkar fim itace ta koya mata hakuri, zama da mutane, da kuma kai zuciya ne sa da a da bata da su.
Jaruma Halima Ibrahim ta ci gaba da cewa ita yanzu har iyayen ta ma dai mamakin kyawawan halayen ta suke yi tun bayan shigar ta harkar fim din gadan-gadan.
Tun farko dai jarumar ta bayyana cewa ta dade tana sha'awar harkar ta fina-finan tun tana karama amma bata fito ta fadawa iyayen ta ba sai da ta kammala karatun ta na Digiri a jami'a.
Post a Comment
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.