Mutane da dama su kan ji tsoron sayen zuma saboda ba sa iya banbance mai kyau da wacce aka yi wa algus.

Akwai hanyoyi daban daban masu sauki da ake amfani da su wajen gane zumar da aka gurbata kamar haka:

1. Gwajin ruwa
Zuma mai kyau ba ta narkewa da zaran an zuba ta a cikin ruwa, za ta tafi kasan ruwan ne ta kwanta yayin da mai algus da zaran an zuba ta a ruwa za ta gauraye da ruwan.

2. Gwajin Ashana
Idan aka dangwala ashana a cikin zuma mai kyau aka kyasta ta za ta kunnu ba tare da matsala ba yayin da zuma mai algus za ta hana ashanar kunnuwa.

3. Kwajin Biredi
Idan aka shafa zuma mai kyau akan biredi, biredin ba ya laushi sai dai ya kara tauri, yayin da biredin zai nadi zumar kamar yadda yake nadar ruwa sannan ya yi laushi idan ba mai kyau ba ce.

4. Gwajin Kwanduwa
Idan aka zuba zuma mai kyau akan kwanduwar da aka fitar da ita daga cikin danyen kwai aka gauraye su tare, za a ga kwanduwar ta koma kamar an dafa. Zuma mai algus kuwa ba ta da wani tasiri akan kwanduwa.

Baya ga wadannan hanyoyi hudu, mutum zai iya gano zuma mai kyau daga dandano da kamshin ta. Zuma ba ta daci daci ko kauri a baki sai dai idan an hada ta da narkakkiyar suga.

Post a Comment

 
Top