Wani Sabon Fim Din TuranciBikin kaddamar da sabon shirin Fim din Turanci mai suna ‘Big Island Ghost’ (BIG) ya samu halartan manya manyan jaruman fina finan Najeriya a jihar Legas, inji rahoton Daily Trust.
A yayin taron an jin jina tare da yaba ma jarumin Kannywood Ali Nuhu saboda rawar daya taka cikin wannan kayataccen Fim, inda majiyar Arewarmu ta jiyo fitacciyar jaruma Rahama Sadau tana yaba masa da kanta.
Baya da yabo da Rahama Sadau tayi ma Ali Nuhu, ta watsa hotunan taron a shaukan ta na sadarwa don jin dadin masoyan fina finan Kannywood.
Wannan Fim mai suna BIG anyi shi ne akan wani mutumi daya mutu amma ya dawo a fatalwa saboda wai bashi da abokiyar zaman a barzahu, kuma shahararren mai bada umarni BB Sasore ne kula da Fim din, sai Omorinsojo da Olusoga suka shirya shi.
Manyan jarumai irin su Ali Nuhu, Tomiwa Edun,Chigurl, Saidi Balogun, Lala Akindoju, Akah Nnani, Uche Jombo, Damilola Adegbite, Dorcas Fapson, Ozzy Agu, Lord Frank, Makida Moka da Bimbo Ademoye sun samu halartan bikin.

Ali nuhu wlh kaji tsoron Allah, akullumfa kara tsufa kakeyi, kamata yayi ace yanzu kakoma tuburan, amma kaqi, al:adar turawa take burgeka, har kana iqirarin wai sana'a ce kakeyi, Allah udan baka gyaraba akwai matsala, Allah yasa mugane.
ReplyDelete