"Bayan wani lokaci hakan al'amarin ya kasance, ko me ke faruwa a nan? Ina son mijina, mun yi auren jin dadi, tare da samun kyawawan 'ya'ya; ko me ke faruwa?"
Matsalar ta sha'awa ce. Duk da cewa mafi yawan mutanen da suka dade da aure za su tabbatar da cewa karsashin sha'awa kan dusashe tsawon lokaci, Gattuso ba ta ma da sha'awar tarawar jima'i ko kadan. Ba ma ga mijinta kadai ba; ba ta ma sha'awar kowa.
Masana tantance tasirin kwakwalwa kan dabi'ar jima'a sun yi ikirarin cewa irin wannan sauyin bijirowar sha'awar jima'i al'amari ne da aka saba gani, musamman ga mata in sun fara tsufa.
Wasu kuwa na ganin raguwar karsashin sha'awa ciwo ne; sakamakon rashin daidaiton sinadarai a kwakwalwa. Ta yiwu yanzu a samu maganin cutar.
A ranakun 3 da 4 ga Yuni, Hukumar kula da ingancin abinci da Magunguna ta Amurka (FDA) za ta tattauna da kwararru su bayar da shawar ko amincewa kwayar Flibanserin a matsayin maganin zaburar da son jima'i na mata "female Viagra" don masu larura su yi amfani da shi ko a jefar da shi a kwandon shara.
Matsalar ta raba kan masana gida biyu, inda wadanda suka amince da masu adawa suka jajirce.
Matsalar kewayar sakonni
Ko mene ne ke kawar da sha'awar jima'i, kuma yaya maganin Flibanserin zai taimaka? Ba mata kadai ne ke kyarar jima'i da sun fara tsufa ba; shaharar gagai samfurin 'Viagra' wani tabbaci ne kan hakan.
A cewar mai barkwanci George Buirns: "Jima'in mai shekara 90 kamar jikqa igiya a ruwa ne." Sai dai yanayin matsalar ya bambanta a tsakanin jinsi (maza ko mata).
Akwai dalilai uku da ke haifar wa mata rashin son jima'i: sha'awa, sha'awa da sha'awa "Akwai maganar da ake fada a likitanci cewa matsaloli uku ne ke kashe sha'awar jima'i karfin mazakuta, karfin mazakuta da karfin mazakuta," a cewar Stephen Stahl, masanin tasirin kwakwalwa kan dabi'u da ke Jami'ar California a San Diego. "Sannan akwai dalilai uku da ke haifar wa mata rashin son jima'i: sha'awa, sha'awa da sha'awa"
Hakikanin abin da ke kashe sha'awa al'amari ne da ya boyu ga masana kimiyya, ko da yake sun fahimci cewa yana da alaka da zagayen sinadarai.
Daya daga mahangar ita ake kira mutuwar gaba ko mazakuta (HSDD) - a mata kuwa ana yi wa lamarin lakabi da dusashewar sha'awar jima'i sakamakon kin kullewar goshin kwakwalwa da ke yin tarin ayyuka a kullum, kamar tunawa da tura sakon ranar haihuwa ko warware matsalolin aiki.
Sakamakon zagayen sinadarai, wadanda ke tarairayar zaburarwa da annashuwa ya kasance a tauye.
Post a Comment
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.