Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ana samun karuwar iyayen da ke yi wa 'ya'yansu fyade a jihar Kano da ke arewacin kasar.
Wata sanarwa da kakakin rundunar a jihar Kano, DSP Magaji Musa Majiya ya aikewa manema labarai ta ba da misalin iyayen da suka rika yin lalata da 'ya'yansu.
"Abu ne da ba a taba tsammani ba a ga uba ya yi lalata da 'yarsa ta cikinsa. Hakan ne ya faru a Unguwa Uku, Kano inda mutumin ya yi wa 'yarsa mai shekara 14 fyade har ya yi mata cikin da aka zubar sau uku", in ji sanarwar.
Magaji Majiya ya kara da cewa sun kama wani mutum da ya yi wa wasu yara mata 'yan biyu masu shekara 13 da kuma kanwarsu 'yar shekara 11 fyade.
Kazalika, a cewar kakakin rundunar 'yan sandan ta jihar Kano, an kama wani mutum dan shekara 25 da laifin yi wa wata 'yar uwarsa fyade sau da dama.
Ya kara da cewa an kama mutum 35 cikin mutum 34 da ake zargi da yin fyade, sannan kuma mutum 36 'yan shekara daga biyar zuwa 13 aka yi wa fyaden.
Ya yi kira ga jama'a da su hada gwiwa da rundunarsa wajen kawar da wannan muguwar dabi'a.
Source: BBC Hausa
Post a Comment