Hukumomi a yankin Banda Aceh na kasar Indonesia sun yanke wa wasu mutum goma bulala 100 kowanen su bisa samunsu da laifin aikata zina karkashin dokokin shari'a na yankin.
Yankin Banda Aceh ta rungumi dokokin shari'a tun bayan lokacinda ta sami kwarya-kwaryan 'yancin kai daga kasar Indonesia a 2001 wadda tayi fama da ta'addanci da ke da asali daga 'yan aware na yankin Banda Aceh lamarinda ya kai ga ba yankin na Banda Aceh kwarya -kwaryan 'yancin kai domin a zauna lafiya.

Wadanda aka yi wa bulala dai har da mata galibi wadanda basu taba yin aure ba.

Kalli hotuna a kasa:

Post a Comment

 
Top