Jarumin yayi wannan ikirarin ne a lokacin da yake fira da majiyar mu da ta tambaye shi ko yaya zai kwatanta fina-finan da ake yi a masana’antar a yanzu da kuma fina-finan da aka yi a da.
Arewaswag ta samu dai ya kada baki yace: “To a hakikanin gaskiya dai ba za’ace ba’a samu ci gaba ba musamman ma ta fannin kayan aiki da kuma yadda ake shirya fim din. Yanzu jarumai da sauran masu ruwa da tsaki duk suna yin sana’ar ne da ilimi ba kamar da ba.”
“Sai dai kuma idan aka koma a bangaren labaran fina-finan yanzu za a samu cewa ba su da ma’ana kuma da yawansu basu wani ilmantar wa kamar na da din.” Ya ce.
Post a Comment
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.