Shahararriyyar jarumar nan ta wasan fina-finan Hausa na Kannywood watau Hafsat Idris ta bayyana sana'ar fim a matsayin muhimmiyar sana'ar da ta ke rufa mata asiri tare da iyayen ta.

Image © Rumbunkannywood

Jarumar ta yi wannan ikirarin ne a cikin wata fira da tayi da wakilin majiyar mu lokacin da take ansa tambayoyi daga gare shi.

An samu labarin cewa jarumar dai ta fara fim ne a watan Disambar shekarar bara ta 2016 sannan kuma dalilin yin fim din nan nata na Barauniya ya sa masu hada fina-finai na yin ruguguwar sanya ta a fina-finansu saboda yadda ta kware a lokaci guda.

Haka ma dai jarumar ta bayyana cewa kowanne wata takan yin fina-finai akalla 3 zuwa 4 saboda amincewar da furodusoshi suka yi mata wajen taka rawa a manyan fina-finai.

© Naij

Post a Comment

 
Top