Shahararriyar yar fim din dai Hadiza ta yi wannan bayanin ne a wani dan karamin shiri da ta shirya ma masoyanta a shafin ta na sada zumunta na Instagram inda ta ba masoyan ta dama su tambayeta duk tambayar da suke da ita ita kuma ta basu amsa.
NAIJ.com ta samu cewa a wannan lokacin ne tambayoyi daga masoyanta na ta shigowa sai wani ya tambaye ta gaskiyar maganar da yake ji na yawo a masana’antar na cewa tana soyayya da mawakin inda kuma ta ce ba gaskiya ba ne.
A cikin firar ma kuma dai an tambaye ta asalin ta inda ta bayyana mahaifiyar ta a matsayin yar asalin garin Mubi da ke Adamawa sai kuma baban ta dake dan asalin kasar Gabon.
Post a Comment
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.