Rundunar yansanda na jihar Anambra ta damke wani matashi Chukwu Emeka Okafor wadda ya bayar da mahaifinsa,yayansa,kanwarsa da abokansa guda uku na shafin sada zumunta na Facebook bayan ya sauke hotunansu ya je aka wanke masa hotunan da ya gabatar a matsafa domin ayi masa kudi na lokaci daya.
Rahotanni sun nuna cewa bisa bayanai na sirri,rundunar ta kama Chukwu wadda ya yaudari mahaifinsa akan cewa ya bashi kudi domin ya fara sana'a lamarin da yasa mahifinsa ya bashi N100.000 ba tare da sanin cewa Chukwu zai kaiwa matsafi kudinne ba.

Kwamishinan yansanda na jihar Anambra CP Garba Baba Umar ya shaida wa manema labarai aukuwar lamarin.Ya kuma kara da cewa rundunarsa zata gurfanar da Chukwu a gaban Kotu bayan ta kammala bincike.

Post a Comment

 
Top