Cibiyar nazarin harkokin bincike da bunkasar kasa ta NASRDA (National Space Research and Development Agency) ta bayyana wasu jihohi hudu na kasar nan gami da babban birnin tarayya na Abuja da girgizar kasa ka iya aukuwa cikinsu.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, jihohin da ka iya fuskantar wannan mummunar barazana ta girgizar kasa sun hadar da Kaduna, Bayelsa, Ogun da kuma Oyo.

Shugaban wannan cibiya ta NASRDA, Farfesa Sa'idu Muhammad, shine ya bayyana hakan a yayin halartar wani babban taro na kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya da aka gudanar cikin babban birnin kasar nan na tarayya yau Alhamis.

A tsakanin ranakun 5 zuwa 7 ga watan Satumba aka fuskanci aukuwar girgizar kasa cikin garin Abuja, inda bincike ya tabbatar da cewa wannan lamari ya auku ne a sakamakon yawan haka rijiyoyin burtsatsai da adadin su ya kai 110, 000 da kuma yasar ruwa mai tarin yawa daga cikin su.

Kazalika tarihi ya bayyana cewa, girgizar kasa ta auku cikin garin Ijebu dake jihar Oyo a shekarar 1984, inda shekaru biyu da suka gabata kuma ta auku a jihohin Bayelsa da Kaduna.

A halin yanzu akwai yiwuwa tarihi zai maimaita kansa cikin wannan jihohin sakamakon bincike na kwana-kwanan nan da cibiyar ta NASRDA ta gudanar bayan aukuwar lamarin a yankin Mpape dake garin Abuja.

A sanadiyar haka Farfesa Sa'idu yake kira ga gwamnatin tarayya akan ta mike tsaye wurjanjan domin tunkarar wannan mummunar annoba da muddin ba a farga ba sai ta auku cikin jihohin da binciken su ya tabbatar.
Naija.ng

Post a Comment

 
Top