Hukumar kwallon kafa ta kasashen Turai, UEFA, ta ce za’a fara amfani da fasahar taimakawa alkalin wasa da maimaicin bidiyo, a gasar zakarun turai ta kakar 2019/2020, da kuma gasar cin kofin kasashen nahiyar turai da za a yi a shekarar 2020.

A cewar hukumar ta UEFA a kakar wasa ta 2020 da 2021, za soma amfani da fasahar taimakawa alkalin wasan, a gasar Europa da kuma ta cin kofin UEFA, wato Super Cup.

Matakin UEFA na amincewar amfani da fasahar maimaicin bidiyon a wasannin da take shiryawa, ya biyo bayan nasarar amfani da fasahar da aka samu yayin gasar cin kofin duniya ta bana da Rasha ta karbi bakunci.
RFIhausa.

Ko menen Ra'ayinku ?

Post a Comment

 
Top