Jam'iyyar APC tana gudanar da tantancewar a Makarantar Pramare na Kauran Gwandu da ke Makerar Gandu, ita PDP tana gudanar da nata a garin Gwadangaji.
Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kebbi Arch.Bala Sani Kangiwa, ya shaida mana cewa "Gwamna Atiku Bagudu ne kadai dan takara tilau da Jam'iyyar APC ta tsayar".
Bayananin shugaban jam'iyyar APC ya kawar da jita-jita da ke zagayawa har da rudani kan lissafin nazari ga jama'a ko miye sahihin matsayin dan takarar kujerar Gwamna a jam'iyyar APC Alh. Ibrahim Mera Chiroman Kabbi kan wannan takara ta kujerar Gwamnan jihar Kebbi. Kuma wadannan kalamai na Arch.Bala Sani Kangiwa sun warware kunshin kayan Koli domin kowa ya gan abinda ya kunsa.
Yunkuri da muka yi domin samun Alh.Ibrahim Mera ta wayar Salula domin jin ta bakinsa a kan wannan lamari ya ci tura, domin dai bai amsa kiraye kiraye da muka yi masa ba kafin mu rubuta wannan rahotu.
Wata majiya ta rada mana cewa, nan da dan lokaci kadan bayan tantance Wakilai, za a je babban Filin wasa na Haliru Abdu, domin amincewa da Gwamna Atiku Bagudu a matsayin dan takara na jam'iyar APC a jihar Kebbi.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Post a Comment
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.